Romans 7

Misali Daga Aure

1Ba ku sani ba, ʼyanʼuwa-ina magana ne fa da mutanen da suka san doka-cewa dokar tana da iko a kan mutum muddin yana a raye ne kawai. 2Misali, bisa ga doka mace mai aure tana ɗaure ga mijinta muddin mijin yana da rai, amma in mijinta ya mutu, an sake ta ke nan daga dokar aure. 3Saboda haka fa, in ta auri wani yayinda mijinta yana raye, za a ce da ita mazinaciya. Amma in mijinta ya mutu, an sake ta ke nan daga wannan doka, ita kuwa ba mazinaciya ba ce, ko da yake ta auri wani.

4Saboda haka ʼyanʼuwana, ku ma kun mutu ga dokar ta wurin jikin Kiristi, domin ku zama na wani, gare shi wanda aka tashe shi daga matattu, don mu ba da amfani ga Allah. 5Gama saʼad da halin mutuntaka yake mulkinmu, shaʼawace-shaʼawacen zunubi waɗanda dokar ta zuga sun yi ta aiki a jikunanmu, don mu ba da amfani wa mutuwa. 6Amma yanzu, ta wurin mutuwa ga abin da dā ya ɗaure mu, an sake mu daga dokar saboda mu yi hidima a sabuwar hanyar Ruhu, ba a tsohuwar hanyar rubutaccen ƙaʼida ba.

Yin Fama da Zunubi

7Me za mu ce ke nan? Dokar zunubi ce? Sam, ko kaɗan! Hakika ai, da ban san mene ne zunubi ba in ba ta wurin doka ba. Gama da ban san mene ne ƙyashi yake ba tabbatacce in ba don doka ta ce, “Kada ka yi ƙyashi ba.”
Fit 20.17; M Sh 5.21
8Amma zunubi, da ya sami dama ta wurin umarnin nan, ya haifar a cikina kowane halin ƙyashi iri-iri. Gama in babu doka, zunubi matacce ne. 9Dā kam ina da rai saʼad da ban san doka ba; amma da umarni ya zo, sai zunubi ya zaburo da rai na kuma mutu. 10Na gane cewa wannan umarnin da aka nufa ya kawo rai, a gaskiya ya jawo mutuwa ce.

11Gama zunubi, da ya sami dama ta wurin umarni, sai ya ruɗe ni, kuma ta wurin umarnin kuwa ya kashe ni. 12Saboda haka fa, dokar tana da tsarki, umarnin kuma yana da tsarki, su duka suna da adalci da kuma kyau. 13Abin nan da yana mai kyau, zai kawo mini mutuwa? Ko kaɗan! Amma domin zunubi ya bayyana kansa a matsayin zunubi, sai ya haifar da mutuwa a cikina ta wurin abin da yake mai kyau, domin ta wurin umarnin nan zunubi ya fito da matuƙar muninsa.

14Mun san cewa doka aba ce ta ruhu; amma ni ba na ruhu ba ne, an sayar da ni a matsayin bawa ga zunubi. 15Ban gane abin da nake yi ba. Don abin da nakan so yi, ba shi nakan yi ba, sai dai abin da nake ƙi, shi nake yi. 16In kuma na yi abin da ba na son yi, na yarda da cewa dokar aba ce mai kyau. 17Kamar dai yadda yake, ba ni kaina nake yinsa ba, sai dai zunubin da yake zaune a cikina ne. 18Gama na san cewa babu wani abin kirkin da yake zaune a cikina, wato, a mutuntakata.
Ko kuwa jikina
Gama shaʼawar yin abu mai kyau kam ina da ita, sai dai ikon yin ne fa babu.
19Gama abin da nake yi ba shi ne abu mai kyau da nake so in yi ba; aʼa, mugun da ba na so in yi-shi ne nake ci gaba da yi. 20To, in na yi abin da ba na so in yi, ba ni ba ne nake yinsa, sai dai zunubin nan da yake zaune a cikina.

21Saboda haka na gane wannan ƙaʼida ce take aiki a cikina: Saʼad da nake so in yi abu mai kyau, sai in ga cewa mugun nan ne nake yi. 22Gama a ciki-cikina ina farin cikin da dokar Allah; 23amma ina ganin wata doka tana aiki a gaɓoɓin jikina, tana yaƙi da dokar hankalina, tana kuma sa in zama ɗaurarren dokar zunubin da take aiki a gaɓoɓin jikina. 24Kaitona! Wane ne zai cece ni daga wannan jiki mai mutuwa? 25Godiya ga Allah-ta wurin Yesu Kiristi Ubangijinmu!

Saboda haka fa, ni kaina a cikin hankalina, ni bawa ne ga dokar Allah, amma a mutuntaka, ni bawa ne ga dokar zunubi.

Copyright information for HauSRK